الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر، " سبحان الذي سخر لنا هذا وما كنا له مقرنين * وإنا إلى ربنا لمنقلبون " ((اللهم إنا نسألك في سفرنا هذا البر والتقوى، ومن العمل ما ترضى، اللهم هون علينا سفرنا هذا واطو عنا بعده، اللهم أنت الصاحب في السفر، والخليفة في الأهل، اللهم إني أعوذ بك من وعثاء السفر، وكآبة المنظر، وسوء المنقلب في المال والأهل))، وإذا رجع قالهن وزاد فيهن: ((آيبون، تائبون، عابدون، لربنا حامدون)).
Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma. "Tsarki ya tabbata ga wanda Ya hore mana wannan, alhali ba mu kasance masu iya rinjayar sa ba, kuma lallai mu, zuwa ga Ubangijinmu, masu komawa ne." (Ya Allah, muna roƙonKa biyayya da taƙawa a cikin wannan tafiyar tamu, da ayyukan da Kake yarda da su. Ya Allah, Ka sauƙaƙa mana wannan tafiyar tamu, Ka kuma naɗe mana nisanta. Ya Allah, Kai ne Abokin tafiya, kuma Mai kula da iyalin da aka bari. Ya Allah, ina neman tsarinKa daga wahalhalun tafiya, da sauyin [hali] mai baƙin ciki, da mummunan komowa a cikin dukiya da iyali.) Idan kuma ya dawo, yakan faɗi irin haka ya ƙara da: (Muna dawowa, muna masu tuba, masu bauta, masu godiya ga Ubangijinmu.)
Danna don ƙirgawa

