يجمع كفيه ثم ينفث فيهما فيقرأ فيهما: بسم الله الرحمن الرحيم " قل هو الله أحد * الله الصمد* لم يلد ولم يولد* ولم يكن له كفوا أحد ". بسم الله الرحمن الرحيم " قل أعوذ برب الفلق* من شر ما خلق* ومن شر غاسق إذا وقب* ومن شر النفاثات في العقد* ومن شر حاسد إذا حسد ". بسم الله الرحمن الرحيم " قل أعوذ برب الناس* ملك الناس* إله الناس* من شر الوسواس الخناس* الذي يوسوس في صدور الناس* من الجنة و الناس " ثم يمسح بهما ما استطاع من جسده يبدأ بهما على رأسه ووجهه وما أقبل من جسده (يفعل ذلك ثلاث مرات).
Ya kasance yana haɗa tafukan hannayensa, sannan ya yi tofi a cikinsu, ya karanta a cikinsu: Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. "Ka ce, Shi ne Allah, [Wanda yake] Makaɗaici, Allah, Wanda ake nufa da buƙata. Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba, kuma babu wani da ya kasance tamka a gare Shi." Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. "Ka ce, Ina neman tsari ga Ubangijin safiya, daga sharrin abin da Ya halitta, da daga sharrin dare idan ya yi duhu, da daga sharrin masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle, da daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada." Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. "Ka ce, Ina neman tsari ga Ubangijin mutane, Mamallakin mutane, Abin bautawar mutane, daga sharrin mai sanya waswasi mai ɓoyewa, wanda yake sanya waswasi [na sharri] a cikin ƙirazan mutane, daga aljanu da mutane." Sannan ya shafa da su abin da zai iya kaiwa na jikinsa, yana farawa da kansa da fuskarsa da gaban jikinsa (yana yin haka sau uku).
Danna don ƙirgawa

