قال النبي صلى الله عليه وسلم ((إذا كان جنح الليل – أو أمسيتم – فـكفوا صبيانـكم، فإن الشياطين تنتشر حينئذ، فإذا ذهب ساعة من الليل فخلوهم، وأغلقوا الأبواب واذكروا اسم الله؛ فإن الشيطان لا يفتح بابا مغلقا، وأوكوا قربكم، واذكروا اسم الله، وخمروا آنيتكم، واذكروا اسم الله، ولو أن تعرضوا عليها شيئا، وأطفئوا مصابيحكم)).
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Idan dare ya yi — ko idan kun shiga maraice — ku riƙe 'ya'yanku kusa da ku, domin shaiɗanu sukan bazu a wannan lokaci. Sannan idan sa'a ɗaya ta dare ta wuce, ku sake su, ku rufe ƙofofi kuna ambaton sunan Allah, domin Shaiɗan ba ya buɗe ƙofar da aka rufe. Ku ɗaure salkunanku kuna ambaton sunan Allah, ku rufe kwanukanku kuna ambaton sunan Allah — ko da wani abu kawai za ku ɗora a kan bakinsu — ku kuma kashe fitilunku."
Danna don ƙirgawa

