Sirar AnnabiAnnabi ﷺ ya yi kira zuwa Musulunci a ɓoye kusan shekara uku, saboda tsoron zaluncin Ƙuraishawa. Na farkon waɗanda suka yi imani da shi su ne magabatan muminai: Khadijatu, da Abubakar, da Aliyu, da Zaidu ɗan Harisa, sannan mutane suka shiga addinin ɗaiɗai. Ya mai da gidan Al-Arƙam ɗan Abil Arƙam cibiyar koyar da Musulmi da karatun Alƙur'ani a ɓoye.

